Amfanin Zuma Da Girfa

by Abrahamjr


Health & Fitness

free



AMFANIN ZUMA GA DAN ADAMZuma wani irin abinci ne mai zaki kamar shigen suga wanda kudan-zuma ke samarwa daga furen itace ko shuka -wato wani romon sinadari dake cikin furen itace ko shuka da kudan-zuma ke tsotsowa (nectar) domin sarrafa ruwan zuma. Mutane na amfani da zuma a matsayin abinci ko magani. Sabili da muhimmancin zuma, a cikin surorin Alqurani maigirma - akwai surah mai sunan kudan zuma - wato Surat An- Nahl. Allah (S.W.A.) ya bayyana mana muhimmancin zuma ga rayuwar dan adam a cikin wannan surah " ...waraka ce ga mutane." (An Nahl: 69). Hakika kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya bayyana mana muhimmancin ta a wasu hadisai.Don haka, zuma nada amfani ga lafiya kamar haka:1. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.2. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.3. Tana taimaka ma mai-mura, tari , atishawa da sauran matsalolin sanyi.4. Maganin gudawa ce.5. Maganin gyambon ciki - Ulcer.6. Tana karfafa garkuwar jiki.7. Tana rage hadarin kamuwa daga cututtukan zuciya, musamman idan aka hadata da Kirfat (cinnamon).8. Tana sanya kuzari a jiki.9. Tana rage nauyin kiba. Shan ruwa mai-`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage `kiba.10. Tana saukaka narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.11. Tana rage kumburi mai sanya waje yayi kalar ja da radadin ciwo.12. Tana kyautata lafiyar kwalwa.* Amfanin Zuma* Amfanin Girfa (Cinnamon Powder)* Honey* Cinannamon Powder* Menene Cinnamon Powder a Hausakada ku manta kuyi rate na wannan app13. Tana gyara fata da rage kurajenfuska (pimples) idan ana shafa ta.